Mummunar ambaliyar ruwa ta afkawa jihar Neja

Mummunar ambaliyar ruwa ta afkawa jihar Neja

Sama da garuruwa 62 ne ambaliyar ruwan sama tayi awon gaba da su a jihar Neja dake tarayyar Najeriya, duk da yake dai babu asarar rayuwa amma ambaliyar ruwan ta jefa dinbim mutane cikin damuwar rashin muhalli.

Mummunar ambaliyar ruwa ta afkawa jihar Neja
Mummunar ambaliyar ruwa ta afkawa jihar Neja
Mummunar ambaliyar ruwa ta afkawa jihar Neja
A car being 'swallowed' by the flood on the street Photo: O. Emmanuel

Amliyar ruwan da ta faru a kananan hukumomin Idati da Makwa mai makwabtaka da madatsun ruwan Kayinji da Jaba, ta jefa dubban Jama’a cikin mawuyacin hali na rashin muhalli da kuma barazanar barkewar cututtuka.

Kamar yadda daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa Alhaji Hassan Dan Masani daga kauyen ketso, yace yanzu haka shi da yara da mata sunkai su arba’in suna tsugunne cikin tamfol guda, inda kuma yace suna bukatar magunguna.

A halin da ake ciki dai yanzu hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja ta kai agajin kayan abinci da adadin kudinsu ya kai Naira Miliyan 61. Shugaban hukumar bada agajin Alhaji Ibrahim Inga, yace sun riga sun kai ajin farko na agaji, aji na biyu kuma ana ran zuwa ranar Laraba zai isa in Allah ya yarda.

A wani labarin kuma mutum guda ya rasa ransa, a unguwar Kitirku dake cikin garin Minna, alokacin da ruwan sama mai karfi yayi awon gaba da motar da yake ciki, yayin da yake kokarin tsallaka rafin dake unguwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel