Masoya sunyi baiko bayan soyayyar shekaru 10

Masoya sunyi baiko bayan soyayyar shekaru 10

- Adenike da Oluwaseun wasu ma’aurata ne da sukayi yawo a kan shafin Instagram

- Adenike ta bayyana baikonta ta kuma bayyana yadda suka dauki tsawon shekaru 10 suna soyayya

Masoya sunyi baiko bayan soyayyar shekaru 10
Adenike da Oluwaseun

Wasu ma’aurata sunyi yawo a shafin zumunta na Instagram saboda labarin soyayyarsu. Macen da aka kira da Adenike da saurayinta, Oluwaseun, ya nemi yardan auranta a jiya 10 ga watan Oktoba. Labarin soyayyar tasu ne yasa kowa ke Magana a kansu.

Adenike ta bayyana cewa sun dauki tsawon shekaru 10 suna soyayya kuma lokacin tana da shekaru 17 a duniya. A yanzu, masoyan biyu sunyi baiko kuma suna shirin yin aure nan ba da jimawa ba. Kalli hoton a kasa:

KU KARANTA KUMA: Motan yan fashi yayi hatsari

Masoya sunyi baiko bayan soyayyar shekaru 10
zoben baikon Adenike

Ta ce: “Ina da shekaru 17 kawai lokacin da na hadu da kai Oluwaseun, ban san komai ba game da soyayya, kai ka koya mun soyayya, ka gina ni tun ina yar karamar yarinya har na zama cikakkiyar mace a yau. Mun fuskanci kalubalancin rayuwa tare, lokacin da mutane ke kiran yan matansu da sunaye masu dadi, kai kana kirana fitinanniyar yarinya (baby terror).”

KU KARANTA KUMA: Buhari a lokacin da yake dalibin makaranta

 “Ina san cewa ina da abun haushi amma duk da haka ka zabe ni. Yanzu na kai tsawon shekaru 10 tare da kai kuma abun kamar jiya muka fara soyayya. Yau da ka dau matakin da ya dace na bukatar na zamo matarka, nayi alkawarin sonka iya karshen rayuwata babu abunda zai raba mu.”

Masoya sunyi baiko bayan soyayyar shekaru 10
Adenike da Oluwaseun

 “Koda dai ina alfahari a koda yaushe cewan bazan taba jin mamaki ba lokacin da zata bukaci hakan, amma duk da haka ka shammace ni. Na wayi gari na ganni sanye da zobena mai kyau na kuma dauka mafarki nake yi har sai da na rufe idanuwa na amma abun da gaske ne.”

 “Ka fi zuma dadi. Idan zaka tambayeni sau da yawa amsar da zan baka shine Eh. Wannan ba irin soyayyar Brad Pitt da Angelina bane. Zai kasance na har abada. Nagode Oluwaseun da ka zabe ni.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng