Mata na cin wuya a Niger Delta
- Sakamakon fashe-fashen bututun Mai a yankin Niger Delta na komawa kan mata da yara a yankin ta hanyar bakar wahala da ke shafar rayuwa da kuma lafiyarsu
- Dagwalon Mai na shafar jama’ar yankin musamman a asibitoci a inda jarirai ke mutuwa, wasu kuma ake haifarsu da mummunan nakasa
Fashe-fashen batutun Mai a Niger Delta da tsagerun yankin ke yi, ya haifar da matsalar lafiya ga jama’a mazauna yankin musamman mata.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, dagwalon Mai a Bodo, da Bomu, da Kpe, da B Dere, da Kdere, da kuma sauran kayukan Ogoni na karamar hukumar Gokana ta jihar Ribas, ya haifar da matuwar jarirai da kuma haihuwar wasu jariran da nakasa.
Duk da cewa dagwalon Mai a sakamkon tsiyayarsa daga ayyukan hakan Man matsala ce, da ta dade a yankin, amma hadarin zama da dagwalon ya fi kamari a yanzu a sakamakon fashe-fashen butun Mai da na iskar Gas da tsagerun ke yi.
KU KARANTA KUMA: Babbar magana! Jami’in sojan ruwa da fasa batutun Mai
Dakta Theophilus Oadgme kwamishinan lafiya na yankin na tabbatar da cewa a watanni uku da suka wuce, asibitoci a yankin sun ga karuwar haifuwar jarirai da ake haifar su da wata nakasa daban-daban, sannan ya kuma ce,
“A wani asibiti a Bori a watanni 8 da suka wuce, sun haifi wasu jarirai da wata naksa irin nakasa mai ta da hankali, daya daga cikin jariran da aka Haifa a 27 na watan Agusta shekarar 2016 na da kankanin kai … A watan Afrilu na shekarar 2016 an haifi wani jariri da kayan cikinsa a waje kan gani saboda fatar cikinsa ba ta karfi, sannan an haifi wani da katon kai a watan Disambam shekara 2015.”
Asali: Legit.ng