Buhari a lokacin da yake dalibin makaranta

Buhari a lokacin da yake dalibin makaranta

Mawallafin littafin Shugaban kasa Muhhamadu Buhari ya bayyana yadda da farko baida ra’ayin zuwa makaranta ko zama dalibi nagari.

A lokacin da mutun ke girma kowa yana da wannan nauyin jihadi na son kasancewa mafi kokari a cikin ajinsu saboda abune da ke sa rai daga garesu, amma ba kowa ke mayar da hankali ga karatunsu ba. Shugaban kasa Muhammadu Buhari na daya daga cikin daiban da basu da ra’ayin karatu, idan dai har abunda mawallafin littafin rayuwar sa John Paden ya rubuta kan rayuwarsa abun bi ne.

Buhari a lokacin da yake dalibin makaranta
Shugaba Muhammadu Buhari tare da John Paden

Farfesa Paden ya rubuta a littafin rayuwar Buhari ‘Muhammadu Buhari: The Challeges of Leadership in Nigeria’, cewa shi dalibi ne dan adawa wanda suka fi son wajen bango hudu na aji.

 “Saboda soyayyarsa ga waje, Buhari ya kasance dalibi mara ji a shekararsa na farko. Sau da yawa yana ketare makaranta gaba daya, ko da dai wannan yana sa malamisu ya zane shi da bulala. Waziri al-Hasan da Mamman Daura ne kawai suka karfafa mai gwiwa har ya mayar da hankali a kan karatunsa.

KU KARANTA KUMA: Patience Jonathan ta koka da hukumar EFCC

Ya rubuta yadda shugaban kasa ya shiryu sosai har ya zama shugaban dalibai a makarantar sa:

“A shekarun farko na makarantar ana koyar dasu a harshen Hausa, daga baya aka fara amfani da harshen Turanci. Buhari ya fara kokari sosai a Turanci, lissafi, da larabci da kuma sauran fanni."

Paden ya yi bayanin cewa shugaban kasa Buhari ya koyi yanda ake shugabanci tun yana da kuruciya.

Wannan ya nuna cewa Buhari yayi kuruciya kamar ko wani mutun ko?

Asali: Legit.ng

Online view pixel