Jam’iyyar PDP tace Shugaba Buhari na buga mulkin Fir’auna

Jam’iyyar PDP tace Shugaba Buhari na buga mulkin Fir’auna

- Jam’iyyar adawa ta Najeriya PDP tace ashe gara Marigayi Janar Sani Abacha da Shugaban kasa Muhammadu  Buhari

- Game da kama manyan Alkalai, PDP tace lallai Najeriya karkashin Shugaba Buhari ta koma bakin mulki na kama-karya

- Babban Lauya Femi Falana yace hakan da aka yi yayi daidai

 

Jam’iyyar PDP tace Shugaba Buhari na buga mulkin Fir’auna

 

 

 

 

 

 

Dangane da kama wasu manyan Alkalan Kasar nan da Jami’an farar kaya na DSS suka yi a a Ranar Asabar dinnan, Jam’iyyar adawa ta Najeriya watau PDP tace ai gara zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha da na Shugaba Buhari. Jam’iyyar PDP tace ko zamanin Soja na Janar Abacha ba ayi irin wannan abu ba.

A wani jawabi da ya samu zuwa hannun mu, Jam’iyyar PDP ta Kasar ta bayyana cewa irin wannan kutsen da aka yi wa Alkalan Shari’a, ko Janar Abacha sai haka. Jam’iyyar PDP tace Shugaba Buhari bai san dokar Kasa da tsarin mulki ba. Jam’iyyar adawar ta zargi Shugaba Buhari da yin katsalandan cikin bangaren Shari’a.

KU KARANTA: Gwamna Fayose ya kara kaca-kaca da Buhari

Jam’iyyar PDP tace yanzu Najeriya ana mulki ne irin na Fir’auna karkashin Shugaba Buhari. Jam’iyyar PDP tace a baya gwamnati ta take shugabannin majalisun Kasar yanzu kuma ta koma kan masu shari’a. Jam’iyyar PDP dai tace a tarihin Najeriya ba a taba samun Shugaban da yayi irin haka ba sai zuwan Shugaba Buhari.

Jam’iyyar adawar kasar jam’iyyar PDP ta ce Shugaba Buhari na buga bakin mulki a Kasa, sai dai Shugaban Kasar ya musanya duk wadannan zargi a jiya. Shugaba Buhari yace da rashawa yake fada ba Alkalai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel