Allah yayi an gano wata yarinya da aka sace
- A jihar Kaduna an gano wata yarinya bayan watanni bakwai da bacewar ta hannun wasu mutane
- An sace Zainab Sultana Umar ne a lokacin da ta bar gida zuwa Islamiya a farkon shekarar nan
- Yanzu haka an kama wadanda suka dauke ta, har suka ce diyar su ce
Wani abin mamaki ya faru a Unguwar Badikko ta Jihar Kaduna, an gano wata yarinya da aka cire tsammanin ta hannun wasu mutane. An sace wannan ‘Yar karamar yarinya mai shekaru kimanin biyar ne a Jajere road da ke Unguwar Badiko a watan Maris za ta je Makarantar Islamiyya.
An sace wannan yarinya mai suna Zainab da ake kira Sultana ne a watan Maris din shekarar nan, har dai iyayen ta sun cire rai.
Asali ma tuni suka maidawa yarinyar da suka haifa sunan wanda ta bace. Sai ga shi kwatsam wani danuwan ta mai suna Malam Umar ya gan ta wajen wata mata Inyamura a garin. Yana kuwa kiran sunan ta, ta amsa. Sai dai wadanda suka sace tan, sun yi karfin halin cewa diyar su ce, su suka haife ta.
KU KARANTA: An kama Shugaban wata Jami'a yaci kudi
Tuni dai Jami’an tsaro suka shiga binciken lamarin, aka wuce da mutanen wajen Hukuma. Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya leka wajen da abin ya faru.
‘Yar yarinyar da aka sace Zainab watau Sultana har ta zama ba ta jin Hausa sai dai irin su yaren Ibo. Wata majiyar ta ce da kyar ma gane iyayen ta, watakila anyi mata asari ne.
Jami’an ‘Yan sanda dai sun kama wannan mutumi da ya sace ta, kuma ana zargin cewa mutumin Adamawa ne, matar sa kuma ana tunani Inyamura ce. A wani faifan bidiyo da ya zo mana, wannan mutumi ya fadawa Jami’an ‘Yan sanda cewa shi ba sa da wani mugun nufi.
Ya ma sa ta a makaranta, ya kuma yi mata fasfo na Kasar waje. Ko da ma can yace shi dan kasuwa ne a Dubai. Yace shi yana sha’awar diya mace, shiyasa da ya gan ta a lokacin, sai yace mata, ta zo, hakan kuwa aka yi. Wasu dai suna cewa sufarar yara yake yi.
Ku kalli bidiyon mai garkuwa da yarinyan yayinda ya tona asiri:
Asali: Legit.ng