Jiga-Jigan malaman Saudiyya sun kawo ma Buhari ziyara

Jiga-Jigan malaman Saudiyya sun kawo ma Buhari ziyara

- Manyan baki sun shigo Najeriya a yau

- Babban limamin Masallacin Madina ya kawo ma Shugaba Muhammadu Buhari ziyara

Jiga-Jigan malaman Saudiyya sun kawo ma Buhari ziyara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tarbi Babban limamin Masallacin Madina,saudiyya a fadar shugaban kasa a yau, juma’a,7 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Ghana ta fara fidda mai zuwa Najeriya da kasashen Afrika ta yamma

Shugaba Buhari ya tarbi gwamnan jihar Zamfara, Abubakar Yari, Babban Limamin Masallacin Madina Sheik Abdul-Muhsin Ibn Muhammad Al-Kasimy, jakadan Saudiyya , Majeed BN Muhammed Algahtamy da Malam Awwal a Aso villa a yau.

Daga cikin jiga-jigan malaman Najeriyan da suka taka ma limamin baya sune, Shugaban Kungiyar JIBWIS, Shaykh Abdullahi Bala Lau; Sakataran Kungiyar JIBWIS,Shayk Muhammad Kabiru Haruna Gombe da sauran su.

Jiga-Jigan malaman Saudiyya sun kawo ma Buhari ziyara

Wasu suna tuhumar Shugaba Buhari da yunkurin musulantar da Najeriya saboda yana nada musulmai a manyan matsayoyi, yana azabtar da mutanen kudu da kuma kashe-kashen da Fulani makiyaya keyi da sauran su.

Shi kuma Shugaba Buhari da yake mutum ne mai basira, bai amsa masu gurnanin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel