AFCON: Duk da ya na jirgi a hanyar dawowa daga Gambia, Buhari ya tuna da Super Eagles
- ‘Yan Super Eagles sun doke kasar Guinea Bissau a gasar AFCON da ake bugawa a kasar Kamaru
- Muhammadu Buhari ya fito ya taya ‘Yan wasan Najeriya murna bayan nasarar da suka samu a jiya
- Shugaban kasar ya yi kira ga tawagar Super Eagles su cigaba da wannan kokari, har su lashe kofin
Cameroon - A ranar Laraba, 19 ga watan Junairu, 2022 ne Najeriya ta buga wasan rukuni na karshe a gasar kofin wasan kwallon kafan nahiyar Afrika.
Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tawagar ‘Yan wasan Super Eagles murna a kan irin nasarorin da suke ta samu a gasar na AFCON 2021.
Da yake jawabi a shafin Facebook, Muhammadu Buhari ya taya ‘yan kwallon kafan Najeriya murnar lashe wasanninsu uku da samun zuwa zagaye na gaba.
“Ina taya Super Eagles dinmu murnar lashe duka wasanninsu uku, da zuwa zagaye na biyu a gasar AFCON cikin salo.”
“Ina kira a gare su, su cigaba da irin wannan kokari, su ma kara kaimin da suka yi wajen zama jagororin rukuninsu.”
“Kuma su dage wajen zama Jakadan Najeriya a filin kwallon kafa da wajen filin wasa.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai kun ci kofi - Buhari
“Daukacin kasar nan ta na sa ran nasara daga gare ku a wasanni bakwai da za a buga har zuwa karshen gasar.”
“An yi uku, saura hudu.” - Muhammadu Buhari
A karshe shugaban Najeriyan ya ce zai cigaba da ba Super Eagles duk wata goyon baya da gudumuwa.
Masu magana a Facebook
Masu bibiyar shugaban kasar a Facebook irinsu Yakson Wudil suka ce ‘Allah ya ba Najeriya sa’a.”
Sai ma mun dauko world cup (kofin Duniya)
- Sabiu Andaza
Super Eagles sun yi matukar kokari.
- Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmaad
Janar bai samun nasara a yaki sai da taimakon sojojinsa. Udumuwar da ka bada ta taimaka sosai wajen wannan nasara.
- Abubakar Aliyu Ahmed
A hanyar dawowa Najeriya
Legit.ng Hausa ta lura shugaba Muhammadu Buhari ya yi wannan magana ne da kimanin karfe 11:00 na dare bayan an tashi wannan wasa a kasar Kamaru.
A daidai lokacin ne jirgin shugaban kasar yake durowa Kaduna daga kasar Gambia inda Buhari ya halarci bikin rantsar da takawarsa Adama Barrow a Banjul.
Asali: Legit.ng