Messi, Lewandowski, Benzema a matsayin manyan gwarazan ‘Yan kwallon Duniya a 2021
- A ranar Litinin, 29 ga watan Nuwamba, 2021, aka bada kyautar Ballon d’Or na shekar nan ta 2021
- Wannan karo ma Lionel Messi ya sake yin zarra, ya lashe Ballon d’Or a karo na bakwai a rayuwarsa
Legit.ng Hausa ta bibiyi wannan biki yayin da aka bada kyaututtuka na musamman ga ‘yan kwallon kafa da kungiyar da suka yi fice a shekarar ta 2021.
Four Four Two tace yayin da Lionel Messi ya zama gwarzo, manyan ‘yan wasan gaban nan; Robert Lewandowski da Karim Benzema su na binsa a baya.
‘Dan wasan tsakiyan kasar Italiya da kungiyar Chelsea, Jorginho shi ne wanda ya zo na uku.
Jaridar tace babu ‘dan wasan Ingila a sahun goma na farko. Raheem Sterling shi ne ya zo na 15, Mason Mount na 19, Harry Kane na 23 sai Phil Foden a 25.
N'golo Kante, Kevin De Bruyne, Mohamed Salah da Cristiano Ronaldo su na cikin ‘yan wasan kungiyoyin kasar Ingila da suka shiga rukunin goman farko.
PSG ta na da mutane uku a sahun farko Lionel Messi, Kylian Mbappe da Gianluigi Donnarumma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jerin sahun farko
1. Lionel Messi (PSG)
2. Robert Lewandowski (Bayern Munich)
3. Jorginho (Chelsea)
4. Karim Benzema (Real Madrid)
5. N'golo Kante (Chelsea)
6. Cristiano Ronaldo (Manchester United)
7. Mohamed Salah (Liverpool)
8. Kevin De Bruyne (Man City)
9. Kylian Mbappe (PSG)
10. Gianluigi Donnarumma (PSG)
Sauran ‘yan wasan da suka yi tashe a bana
11. Erling Haaland
12. Romelu Lukaku
13. Giorgio Chiellini
14. Leonardo Bonucci
15. Raheem Sterling
16. Neymar
17. Luis Suarez
18. Simon Kjaer
19. Mason Mount
20. Riyad Mahrez
Goal.com tace ragowar ‘yan wasan da suka cike mutum 30 su ne: Bruno Fernandes, Lautaro Martinez, Harry Kane, Pedri, Phil Foden. Sai Nicolo Barella, Ruben Dias, Gerard Moreno, Luka Modric da Cesar Azpilicueta.
Asali: Legit.ng