Jihar Zamfara
Ta’adin Halilu Sabubu Buzu ya zo karshe domin sojoji sun hallaka shi, tun a watannin baya aka ji jami’an tsaro su na cigiyar Halilu Buzu domin a kashe shi.
Gawurtaccen ɗan bindigar nan, Bello Turji ya yi magana kan tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isah Pantami, ya ce yana da wazinsa da ya ji yana kafirta gwamnati.
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa akwai makarkashiya a lamarin tsaron jihar kowa ya sani kuma wasu ne manya a sama da ke siyasantar da shi domin bukatunsu.
Sojojin Najeriya sun kashe mai gidan Bello Turji, Kachalla Halilu Sububu da wasu jiga jigan yan ta'adda a Zamfara. An kashe Dangote, Baleri da Modi Modi da Damina.
Gawurtaccen ɗan bindigar nan da ya addabi al'ummar Zamfara, Bello Turji ya tabbatar da cewa ya sa harajin N50 kan mutanen garin Moriki a yankin Shinkafi.
A yayin da jam'iyyar APC ta zargi gwamnatin PDP mai mulki a Zamfara da gaza kawo karshen ta'addanci, ita ma gwamnatin jihar ta yiwa APC zazzafan martani.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hare-hare a jihar Zamfara da safiyar ranar Alhamis. 'Yan bindigan sun hallaka jami'an sojoji uku bayan sun bude musu wuta.
Matasan garin Moriki da Bello Turji ya ce zai kashe sun tsere cikin dare. Dan ta'addar ya ce zai kashe su ne idan ba a kawo masa kudi N30m daga garin Moriki ba.
A martaninsa a shugaban 'yan ta'adda, Bello Turji, Bulama Bukarti ya yi nuni da cewa Turji ya dage da fitar da bidiyo kwanan nan saboda wasu manyan dalilai guda uku.
Jihar Zamfara
Samu kari