Jihar Zamfara
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar wani hatsari wanda ya lakume rayukan wasu mutane shida 'yan gida daya. An ce mota ce ta kwacewa direba.
A wannan labarin, za ku ji cewa wani dan bindiga, Kachalla Gajere ya kashe rikakken jagoran yan ta’adda, Kachalla Tsoho Lulu a wata arangama da ta afku a Zamfara.
A wani harin kwantan bauna na ramuwar gayya, yaran marigayi Kachalla Nagala sun halaka hatsabibin dan bindiga, Kachalla Mai Shayi da ke dabar Kachalla Mai Bille.
Kungiyar masu kishin jihar Zamfara sun karyata labarin fara zaman kotu kan zargin tsohon gwamnan jihar, Dr. Bello Matawalle da alaka da ta'addanci.
Yan bindiga sun kai wani mummunan hari a yankin Janboka da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara inda suka sace mutane 40 da hallaka wasu guda biyu.
Hukumar NSCDC ta nuna takaicinta kan samun jami'inta da aikata laifin safarar makamai da kwayoyi ga 'yan bindiga a jihar Zamfara. Ta shirya korarsa.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya za su ci gaba da kai hare hare kan miyagun 'yan bindiga.
Kungiyar Arewa Peace Foundation (APF) ta fito ta nuna goyon bayanta ga gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal. Ta bukaci mutanen Zamfara su ba shi hadin kai.
Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, ya yi Allah wadai da kalaman da Gwamna Dauda Lawal yake yi kan karamin ministan tsaro Bello Matawalle.
Jihar Zamfara
Samu kari