Jihar Zamfara
Sanatoci daga jihohin Arewa 19 da Abuja, sun jajanta kan rasuwar Sarkin Gumel, Dakta Ahmed Muhammad Sani, CON, da Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman.
Askarawan Zamfara sun kama mutane tara da ake zargi da taimaka wa ’yan bindiga, ciki har da masu ba da bayanai, masu kai kayayyaki da wani likitan ’yan bindiga.
Shugaba Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman, yana yabawa jajircewarsa wajen yaƙi da matsalolin tsaro da samar da zaman lafiya.
Gobara ta tashi a wani bangare na gidan Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal da ke GRA a Gusau, inda jami’an kashe gobara suka garzaya domin shawo kanta.
Gwamna Dauda Lawal ya yi jimamin rasuwar Sarkin Zamfaran Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman, wanda ya rasu a asibitin Federal Medical Centre da ke Gusau.
Sanarwar masarauta ta bayyana cewa Mai Martaba Sarkin Zurmi da ke jihar Zamfara, Bello Suleiman, ya riga mu gidan gaskiya bayan shekara biyar a kan mulki.
Harin 'yan bindiga a babbar hanyar Zamfara ya jefa matafiya a cikin fargaba bayan sace fasinjoji da dama. Abin ya faru ne aan daf da shiga garin Tsafe.
Wani magidanci a Zamfara ya zargi babban jami’in Hisbah da tilasta rabuwar aurensa, sannan ya auri tsohuwar matarsa, yana neman gwamnati ta binciki lamarin.
’Yan sandan jihar Zamfara sun kashe ’yan bindiga 17 bayan musayar wuta, yayin da ake ci gaba da kokarin ceto fasinjojin da aka sace a harin Tsafe.
Jihar Zamfara
Samu kari