Jihar Zamfara
Sojojin Najeriya sun tarwatsa bikin 'yan bindiga da ruwan bama bamai yayin da suke tsaka da bikin aure a dajin Zamfara. An kashe 'yan ta'adda da dama a farmakin.
A labarin nan, za a ji cewa mazauna Zamfara sun shiga tashin hankali bayan wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da basarake jim kaɗan bayan korarsu daga yankin.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani mummunan harin 'yan bindiga a jihar Zamfara. Sojojin sun kuma kwato makamai daga hannun tsagerun.
Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun kai hare-hare kan jama'a a kauyuka daban-daban cikin kwanaki huɗu, ana fargabar sun sace 150.
Ana zargin yaran Bello Turji sun kai hari a wani yanki na Shinkafi a jihar Sokoto. Sun kashe wani matafiyi Yusuf Isah kafin dakarun soji Najeriya su fatattake su.
Mai fashin baki kan lamuran tsaro, Alhaji Sani Shinkafi ya ce tattaunawar da aka yi da Bello Turji ba ta da amfani, inda ya bayyana ta a matsayin rashin adalci.
Wani dan majalisar wakilan Najeriya a jihar Zamfara ya kaddamar da aikin gyaran makabartu. Ya bayyana cewa hakan yana da muhimmmanci ko a addini.
Yayin da ake maganar haɗaka da Bello Turji, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya bayyana damuwa kan yadda ta'addanci ke kara ta'azzara musamman a yankin Arewa.
Jagoran 'yan ta'adda, Bello Turji ya sanar da ajiye makamai bayan zaman sulhu da aka yi da shi a Zamfara. Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunnah ne ya sanar da haka.
Jihar Zamfara
Samu kari