Jihar Zamfara
Labari mai zafi ya zo mana cewa ana tunanin jami'an tsaron Najeriya sun sake yin kuskure. Wannan karo an saki bam da ya kashe mutane da dam dama a jihar Zamfara.
Yayin da sojoji ke ci gaba da kai farmaki kan yan bindiga, an ce shugaban yan ta'adda, Ado Aliero ya rikice gaba daya inda yake gudu ƙauyuka daban-daban.
Rahotanni sun tabbatar an gano dan ta'adda Bello Turji da yaransa sun kwana suna dasa wasu abubuwa a kusa da duwatsun Fakai da Manawa don kare kansu daga hare-hare.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan mutanen da ke garin Gana a jihar Zamfara, 'Yan bindigan sun yi garkuwa da mata da kananan yara.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun taso mutanen wasu kauyukan jihar Zamfara a gaba. Tsagerun 'yan bindigan sun sanya harajin N172m kan kauyukan da ke Tsafe.
Jami’an tsaro sun kashe Sani Rusu, ɗan ta’addar Fulani a Tsafe a yayin wani samame, tare da ƙoƙarin kamo abokinsa, dillalin ƙwayoyi, Shamsu Danmali.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu yan daba sun kai farmaki kan jigon APC a jihar Zamfara, Dr. Sani Shinkafi bayan ya soki ayyukan ta'addanci na Bello Turji.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi wa motar fasinjoji kwanton bauna a jihar Zamfara. 'Yan bindiga sun ta sa keyar dukkanin fasinjojin zuwa cikin daji.
Shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, ya yi kunnen uwar shegu da rokon da wasu shugabannin Fulani suka yi masa. Ya ci gaba da kai hare-hare a Zamfara.
Jihar Zamfara
Samu kari