Yar Makaranta
Wata dalibar aji hudu a jami’ar jihar Kwara, Malete da ke karamar hukumar Moro, mai suna Rashidat Shittu, ta dauki ranta da kanta saboda ta samu matsala a karatunta.
Dalibai biyu na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi, Lokoja sun mutu sakamakon shakar hayakin da ke fitowa daga janareta da ke kusa da tagar dakunansu.
'Yan sanda sun fara bincike bayan mutane sun gano gawar wata daliba 'yar aji 3 a kwance cikin jininta a dakinta da ke jami'ar AAUA a jihar Ondo, an fara bincike.
Ana fama da kudin man fetur a wajen kai yara karatun boko, Nyesom Wike ya kara haraji. Karin kudin da aka yi zai fara tasiri ne daga watan Junairun 2024.
Wata daliba mai suna Jamima Shetima Balami ta dauki ranta ta hanyar shan wani abu da ake kyautata zaton gubar bera ne a jihar Adamawa bayan rabuwa da saurayinta.
Lola Bowoto, wata 'yar Najeriya da ke karatu a jami'ar kasar Ingila, ta shiga shafukan sada zumunta inda ta nemi taimakon mutane domin ta biya ta kudin makaranta.
Bidiyon wata yarinya yar makaranta ya dauki hankula, bayan an nuna ta tana yin sallah a kan hanya. Yarinyar ta yi amfani da jakarta a matsayin tabarma.
A wani abin nuna godiya ta samun ilimi, wani dalibi ya ba tsohon malamin sa kyautar sabuwar a jihar Anambra. Ya kuma ba shi kyautar N100,000 ya sha mai.
Gwamna Agbu Kefas ya ce nan gaba kadan za a dakatar da daukar masu kwalin NCE aikin koyarwa a jihar Taraba, sai kana da kwalin digiri na daya ko na biyu.
Yar Makaranta
Samu kari