Yar Makaranta
Gwamnatin Gombe ta umarci makarantun jihar su kulle zuwa ranar Juma'a. An umarce su da su yi jarrabawa cikin gaggawa domin sallamar dalibai saboda barazanar tsaro
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin Bauchi ta ce a rufe makarantun firamare, sakandare da na gaba da sakandare mallakkinta da masu zaman kansu saboda sace dalibai.
Dalibai 50 daga makarantar St. Mary’s Papiri sun tsere daga hannun ’yan bindiga a Niger, yayin da daruruwan sauran dalibai da ma’aikata ke tsare a daji.
Yara sun fara barin FGGC Bwari bayan umarnin gwamnati na rufe makarantu 47 saboda barazanar tsaro da yawaitar sace dalibai a Arewa. Iyaye sun yi martani kan hakan.
Jerry Gana ya ce 'yan bindiga na amfani da dalibai a matsayin garkuwa bayan barazanar Trump, yana kira ga gwamnati ta karo haɗin gwiwa da ƙasashen waje.
Yobe ta rufe dukkan makarantun kwana a matsayin matakin kare ɗalibai bayan karuwar garkuwa da su a jihohi kamar Kebbi da Neja. Jihohi da dama sun bi sahu.
Karamin Ministan Tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya bukaci al'umma su bai wa jami'an tsaro hadin kai yayin da ake dab da kubutar da dalibai matan Kebbi.
Makarantar St Mary Papiri da ke jihar Neja ta fitar da bayani cewa adadin daliban da aka sace a harin 'yan bindiga ya kai 303 bayan an nemi dalibai 88 an rasa.
Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya yi magana kan sace dalibai da aka yi a jihar Neja. Gwamna Umaru Bago ya ce tun a karon farko an nemi a rufe makarantar.
Yar Makaranta
Samu kari