Albashin ma'aikata
Ma’aikatan shari'a karkashin JUSUN sun rufe kotuna a Ibadan, a wani mataki na yajin aiki. Sun bukaci gwamnati ta kara masu albashi da alawus da 25% da 35%.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya shirya gwangwaje ma'aikata don bukukuwan babbar Sallah. Gwamnan ya umarci a biya su albashin watan Yunin 2025.
Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta fara biyan ma'aikata bashin N35,000 da ta masu alƙawari a watannin baya.
Ma’aikatan hukumar nukiliya sun rufe Ma’aikatar Kudi a Abuja saboda bashin albashi da alawus, sun zargi minista da hana su hakkokinsu duk da roƙon da suka yi.
Gwamna Francis Nwifuru ya ƙara albashi ga sababbin likitoci zuwa N500,000, ya kuma kaddamar da shirin samar da magunguna a farashi mai rahusa a jihar Ebonyi.
Rahoton hukumar kula da albashi na 2007 ya nuna cewa shugabannin kasa na samun fiye da Naira miliyan 10 a kowace shekara, alawus din mazaba kadai na kai N8m.
Jam’iyyar APC ta cire Samad Ogunbo daga takarar shugabancin karamar hukumar Eti-Osa Eta Gabas saboda karɓar albashi sau biyu daga gwamnati lokaci guda.
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa abubuwa guda biyar ne ke lalata albashin ma’aikata a Najeriya, ciki har da tsadar wuta da sadarwa.
Gwamna Okpebholo ya ƙara mafi karancin albashi zuwa ₦75,000 ga ma’aikatan Edo tare da ɗaukar sababbin malamai da ma’aikatan lafiya a fadin jihar.
Albashin ma'aikata
Samu kari