
Albashin ma'aikata







Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 kamar yadda aka yi alƙawari.

Likitocin ARD-FCTA ta gargadi Wike kan yajin aiki mafi muni idan ba a biya bukatunsu ba cikin kwanaki 14, ciki har da albashi, kudin kayan aiki, da gyaran dokoki.

Gwamnaan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya ba shugabannin kananan hukumomi wa'adi domin su biya ma'aikatan da ke karkashinsu hakkokin da suke bin bashi.

Gwamma Douye Diri na jihar Bayelsa ya bai wa ma'aikatan gwamnati hutu daga ranar 24 ga watan Disamba, 2024 zuwa 30 ga wata, ya taya su murnar kirismeti.

Gwamnatin jihar Jigawa ta yi nasarar bankado ma'aikatan bogi masu karbar albashi a jihar. Gwamnatin ta gano ma'aikatan ne a aikin tantancewar da take yi.

Gwamnatin jihar Oyo za ta fara biyan N80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi daga Janairu 2025. Sabon tsarin zai fara daga Yulin 2024 kuma albashin watan 13 na nan.

Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya bayyana cewa ba zai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin N80,000 ba har sai an gama tantance ma'aikata.

Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya janye kansa daga yarjejejniyar da suka yi da kungiyar NLC kan albashi inda ya ce sai ya gama tantance ma'aikata.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya umarci a biya ma'aikatan jihar albashin watan Disamban 2024 da wuri domin bukukuwan da kw tafe.
Albashin ma'aikata
Samu kari