
Albashin ma'aikata







Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake yankewa wasu ma'aikata albashinsu. Ya kafa kwamitin bincike kan lamarin.

Gwamnatin Tarayya ba za ta ci gaba da yakar nauyin bashin jihohi ba. Akanta Janar ta bukaci dakile asarar kudade da rungumar fasahar zamani a lissafin kudi.

Yan kwadago sun fita zanga zangar nuna adawa da korar ma'aikata sama da 3000 a kamfanin rarraba wuta na Ibadan watau IBEDC, sun gabatar da buƙatu 7.

Gwamnatin Najeriya ta shirya daukar ma’aikatan lafiya 28,000 da USAID ke daukar nauyi, domin karfafa kiwon lafiya da rage dogaro da kasashen waje.

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya umarci shugabannin kananan hukumomi su fara biyan mafi karancin albashin N85,000 domin cika ka'idar aiki.

Gwamnatin Dauda Lawal Dare ta bayyana cewa an gudanar da bincike don tantance ma'aikatan jihar a kokarin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin N70,000.

Gwamnonin jihohi 36 za su kashe kudi har N3.87tn kan albashin ma'aikata a shekarar 2025. Hakan na zuwa ne bayan karin albashin N70,000 da aka yi.

Malaman Ebonyi sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani bayan wasu shugabannin kananan hukumomi sun gaza biyan albashin watanni uku na malaman firamare.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da yin kari a shekarun da likitoci da sauran ma'aikatan lafiya suke yi suna aiki. Za su samu karin shekara biyar.
Albashin ma'aikata
Samu kari