Amurka
Wasu daga cikin Amurkawa sun fito zanga-zanga inda suka jaddada adawa da yaƙe-yaƙen da shugabansu Donald Trump ke jefa su a ciki tare da neman a tsige shi.
Wata 'yar majalisar Amurka, Ilhan Omar ta bukaci zama a majalisar kasar domin duba yiwuwar tsige shugaba Donald Trump kan barazanar aikata laifuffukan yaki a Iran.
Farashin mai ya fadi sosai a duniya bayan Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta na makonni biyu, tare da shirin bude mashigar ruwa ta Hormuz.
Iran ta tabbatar da tsagaita wuta da Amurka a yau Laraba, 8 ga Afrilu, 2026, tana mai iƙirarin nasara kan Trump da kuma kare hakkinta na tace nukiliya.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa babu sharadin daina kai hari Lebanon a yarjejeniyar da Iran da Amurka suka yi duk da an ambaci hakan.
Iran ta mika wa Amurka daftarin sulhu da tsagaita wuta mai dauke da sharuda 10, wanda ya haɗa da buɗe mashigar ruwan Hormuz da daina yaƙi a Lebanon da Yemen.
Shugaba Trump ya amince ya dakatar da kai hari kan Iran na tsawon makonni biyu yau Talata, 7 ga Afrilu, 2026, bayan sanya baki da Pakistan ta yi yau.
Shugaba Trump ya yi barazanar ruguza manyan gadoji biyar na Iran, ciki har da Sadr da Lake Urmia, a matsayin dabarun durkusar da tattalin arzikin kasar Iran.
Dakarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun samu nasarar kakkabo makamai masu linzami da jirage marasa matuka na Amurka da Isra'ila yayin da ake ci gaba da yaki.
Amurka
Samu kari