
Amurka







Kasar Amurka ta yi Allah wadai da kisan da wasu 'yan bindiga suka yi wa Rabaran Sylvester Okechukwu kwana daya da sace shi. An kama faston ne a jihar Kaduna.

Wani rahoto ya bankado yadda manyan jami'an gwamnatin Amurka, daga ciki har da tsohon shugaban kasar, Joe Biden su ka taimaka wa Shugaban Binance a Najeriya.

Mata da dama a Najeriya su kan yi korafin cewa manyansu sun nemi lalata da su a wajen aiki, yayin da ake gudanar da bincike, sannan a wanke mazan da ake zargi.

Fitacciyar mawakiya, Angie Stone ta rasu bayan hatsarin mota a Alabama. Ta shahara a hip-hop da R&B, ta kuma bar gagarumar gudunmawa ga duniyar waka.

Ba a sami wata hujja da ke tabbatar da cewa Shugaba Tinubu na korar Amurkawa daga Najeriya ba, kuma babu rahoto kan haramta amfani da wayoyin Amurka.

Kungiyar zaman lafiya ta PeacePro ta nuna adawa da matakin Amurka na shiga yaki da Boko Haram da sauran 'yan ta'addan Afrika. Kungiyar ta ce akwai illoli a lamarin.

Bayan dan majalisar Amurka ya yi tone-tone kan daukar nauyin ta'addanci, tsohon shugaban Kiristocin Najeriya, CAN, Samson Ayokunle, ya ce zargin ya zo a makare.

Kasar Amurka ta bayyana cewa kasarta ta na taimakawa Najeriya da sauran kasashen da suke da bukatar hakan, duk da zargin da ake yi a kan USAID na hannu a Boko Haram.

Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills Jr ya barranta hukumar taimakawa kasashe ta USAID da masaniya a kan wasu ayyukan ta'addancin Boko Haram.
Amurka
Samu kari