Wasar Kwallo
An hura tashi a wasan karshe na AFCON 2023 inda Super Eagles na Najeriya ta fafata Elephants na Ivory Coast, a karshen wasan Ivory Coast ce ta yi nasara.
Jose Mourinho, tsohon kocin Manchester United ya bayyana kasar da ya ke so ta ci gasar AFCON da za a yi a yau Lahadi inda ya ce ya na goyon bayan Najeriya.
'Yan wasan Super Eagles za su samu goyon bayan mataimakin shugaban kasa a wasan karshe na AFCON da ake bugawa a halin yanzu. AN bayyana yadda aka yi.
'Yan jihar Kano na ci gaba da bayyana kokensu a daiai lokacin da aka rasa samun rigar 'yan kwallon Super Eagles a duk fadin jihar yayin da aka zo karshen wasa.
Kyaftin din tawagar Super Eagles, Ahmed Musa ya ce ba ya tsammanin barin kungiyar nan kusa inda ya ce a ko da yaushe ya na shirye idan aka kira shi cikin tawagar.
Fasto Iginla wanda ya yi hasashen nasarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana kan Victor Osimhen, yayin da Najeriya ke shirin karawa da Cote d'Ivoire.
Hukumar kula da kwallon wasan nahiyar Afirika (CAF) ta sanar da cewa dan kasar Mauritania, Dahane Beida, ne zai hura wasan karshe tsakanin Najeriya da Cote d'Ivoire.
A ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu, 2024 za a gwabza wasan ƙarshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka tsakanin Najeriya da masu masaukin baki Ivory Coast.
Fasto Dakta Kan Ebube Muonso ya yi hasashen kasar da za ta lashe gasar AFCON a gobe Lahadi 11 ga watan Faburairu inda ya ce Ivory Coast ce da nasara.
Wasar Kwallo
Samu kari