
Kudu maso gabashin Najeriya







Popoola Joshua, tsohon ɗan takarar NNPP a Oyo, ya koma APC don ƙarfafa jam’iyyar. Tuni Ganduje ya umarci APC ta yi tsare-tsare domin karɓar mulki daga PDP.

Gwamnonin Najeriya sun yi watsi da ƙarin VAT, sun gabatar da sabuwar hanyar rabon haraji don tabbatar da daidaito da kare talakawa, da goyon bayan ci gaban harajin.

Jihohin Kudu maso Yamma na tunkarar barazanar tsaro daga ‘yan bindiga da mayakan ISWAP yayin da DSS ta kama mutum 10 da ake zargi da ta’addanci a shiyyar.

Jam'iyyar PDP reshen jihar Ebonyi ta zaɓi Chidiebere Egwu a matsayin wanda zai maye gurbin mataimakin shugabanta na dhiyyar Kudu maso Gabas, Ali Odefa.

Rahotanni sun nuna cewa wani abin fashewa da aka bayyana a matsayin bom ya tarwatse a loƙacim da mutane ke tsakiyar barci da tsakar dare a jihar Imo.

Gwamna Seyi Makinde ya miƙa sandar mulki ga sabon Alaafin na Oyo, Abimbola Akeem Owoade. An mika sandar ne duk da adawa 'yan majalisar nadin sarki ta Oyomesi.

Gwamna Makinde ya nada Yarima Owoade sabon Alaafin na Oyo, yayin da masu nadin sarauta suka kalubalanci nadin bisa hujjar shari’ar da ke gudana a kotu.

Farfesa Banji Akintoye ya ce Yarbawa miliyan 60 suna goyon bayan neman ƙasar Yarbawa cikin lumana, bisa hakkin cin gashin kai na dokar Majalisar Dinkin Duniya.

Mark Angel ya fuskanci kalubale a 2024, inda ya yi asarar $3.7m wanda ya jefa shi a bashi, sannan ya fuskanci rikice-rikice, amma ubangiji ya ceci rayuwarsa.
Kudu maso gabashin Najeriya
Samu kari