Kudu maso gabashin Najeriya
Muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Alƙali Baba, ya kaddamar da rundunar yan sanda da laƙabin 'Operation Dawo Da zaman Lafiya dole' a yankin kudu-Gabas
Tsagerun Biafra sun hallaka 'yan sanda biyu tare da kone ofishin 'yan sanda a jihar Abia da sanyin safiyar yau Litinin. Wannan shine hari na baya-baya a yankin.
An kame wasu tsagerun Biafra da laifin kashe wani dan sanda tare da yin awon gaba da makaminsa. An kame mutane shida, an kuma tsare su suna jirian hukunci.
Gwamnan jihar Imo ya bayyana korar kwamishinoninsa har 20 daga cikin 28 da ya nada. Sanarwar ta ba zata ta girgiza kwamishinonin, lamarin da bai musu dadi ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da wasu sabbin matakan tsaro ga yankunan kudancin Najeriya. Ya kuma amince da wata takarda kan shan muggan kwayoyi a kasar.
Ƙungiyar inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo, ta ɗau zafi bisa zargin da takewa rundunar sojin ƙasar nan cewa tana tura musulmai yan arewa yankinsu da wata manufa.
Kungiyar BRAC a kudu maso kudu ta bayyana rashin alakarta da ta kusa da ta nesa da haramtacciyar kungiyar fafutukar 'yanta 'yan asalin Biafra. Ba ta goyon baya.
Rundunar yan sandan kasar nan ta samu nasarar cafke mambobin IPOB 16 da ake zargi da kitsa rikice-rikicen da ake samu a yankin kudu maso gabashin ƙasar nan.
Kungiyar gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya sun yanke shawarar yin gemu da gemu da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan bukatar bude filin sauka da tashin jirage a jahar Enugu