Kudu maso gabashin Najeriya
Kungiyar Afenifere ta bukaci kariyar gaggawa ga Farfesa Adeyeye, tana mai cewa barazana a kanta barazana ce ga lafiyar al’umma da tsaron kasa baki daya.
Rundunar 'yan sanda ta kama wani Gbolahan Adebayo bisa zargin kashe budurwarsa da duka a Legas. An dauki gawarta zuwa asibiti domin gudanar da bincike.
Rikicin kabilanci tsakanin mazauna garuruwan Gbelemonti da Maidoti a jihar Edo ya jawo mutuwar mutane 7, tare da jikkata 6. ‘Yan sanda da sojoji sun dakile lamarin.
'Yan bindiga sun harbi fasto tare da sace mutum 6 a wata cocin jihar Delta. Masu garkuwa ba su tuntubi kowa ba, amma jami’an tsaro na kokarin ceto su.
Jam'iyyar LP na ci gaba da rasa jiga-jiganta ga APC da PDP, ciki har da Valentine Ozigbo, dan takarar gwamna, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a Anambra.
PDP ta fara sayar da fom ɗin takarar gwamnan Anambra, zaɓen fidda gwani zai gudana 5 ga Afrilu, yayin da za a mika sunan ɗan takara zuwa ga INEC a ranar 22 ga Mayu.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya jajanta bayan rasuwar shugaba a kungiyar PANDEF, Cif Edwin Clark a yau Talata inda ya ce an yi rashin kishin kasa.
Tsohon ministan yada labaran Najeriya, Edwin Clark ya rigamu gidan gaskiya. An ce jagoran Kudu maso Kudu ya rasu yana da shekaru 97 a daren Litinin, 17 ga Fabrairu.
Rikici ya barke a Osun yayin da APC da PDP suka yi artabu kan dawowar shugabannin APC. An harbe mutane biyu yayin da aka hana Amotekun da 'yan sanda kai dauki.
Kudu maso gabashin Najeriya
Samu kari