Kudu maso gabashin Najeriya
A makon da ya gabata ne aka yanke wa shugaban IPOB, Nnamdi Kanu hukuncin daurin fai da rai, ya shiga jerin wadanda suka wakilci kansu a kotu babu lauya.
Tsohon ministan kwadago, Dr. Chris Ngige, ya bayyana cewa yana nan a raye bayan wasu yan bindiga sun farmake shi a kan wani titi a jihar Anambra.
Wata mata ta rasa rayuwarta bayan ‘yan bindiga sun harbe ta yayin da take ɗaukar bidiyon harin da aka kai wa jerin gwanon motocin Chris Ngige a Anambra.
Shahararren ɗan wasan Nollywood, Odira Nwobu, ya rasu a Afirka ta Kudu yana da shekara 43, lamarin da ya tayar da cece-kuce da alhini a Najeriya.
Wata kotu mai zamanta a Ibadan ta yanke wa wasu mutane biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin kashe direban tasir a rikicin 2024.
'Yan majalisar wakilan Najeriya daga yankin Kudu maso Gabas sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi afuwa ga jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Gwamnonin Kudu maso Yamma sun ce lokacin kafa 'yan sandan jihohi ya yi yayin da suka kaddamar da sabon asusun tsaro domin yaki da 'yan ta'adda da masu laifuffuka.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa ya fara shirin ganin an saki jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu, bayan yanke masa hukunci.
Dangin shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu sun ce akwai makirci na kashe shi bayan kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai kan tuhumar ta’addanci.
Kudu maso gabashin Najeriya
Samu kari