Jihar Sokoto
Yan majalisa sun amince da karya farashin abinci. Za a cigaba da karya farashin abinci a jihar Sokoto bayan amincewar majalisar dokoki, za a sayar da abinci da araha
Mazauna rukunin gidajen Yauri Plats da ke Sokoto sun fito zanga zanga a ranar Talata domin adawa da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na korarsu daga gidajensu.
Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, ya tuna da fursunonin da aka garkame a gidan gyaran hali. Gwamna Ahmed ya yi wa wasu daga cikinsu afuwa.
Rikicin cikin gida na jam'iyyar APC a jihar Sokoto ya sake dagulewa kan wanda zai jagorance ta tsakanin Sanata Aliyu Wamakko da Sanata Ibrahim Lamido.
Alhaji Abdullahi Muhammad Bawa ya yi murabus daga sarauyar Hakimin Sabon Birni a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato, ya bi tsagin Lamido.
Gwamnatin jihar Sokoto ta shirya kaddamar da shirin sayar da shinkafa da sauran kayan abinci bisa farashi mai rahusa. Za a siyar da kayayyaki a mazabun jihar.
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya sanar da rangwamen kaso 55% na farashin shinkafa da wasu kayayyaki domin rage raɗaɗin halin kuncin da ake ciki.
Gwamnatin tarayya ta kara tabbatar da cewa za ta fatattaki yan ta'adda da su ka hana jama'a zaman lafiya, musamman a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.
Shugaban karamar hukumar Isa a jihar Sokoto, Alhaji Sharifu Kamarawa ya tabbatar da cewa Bello Turji na saukewa da nadin dagatai a wasu yankunam jihar.
Jihar Sokoto
Samu kari