Jihar Sokoto
Rahotanni daga jihar Sakkwato sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun yi kwantan bauna, inda suka yi nasarar hallaka gwarazan jami'ai sun kai guda shida.
Jami'an tsaro sun kama Hamza Suruddubu, babban mai safarar makamai ga 'yan bindiga a Sokoto, wanda ake zargi da samar wa Bello Turji da abokan aikinsa makamai.
Jam'iyya mai mulki ta APC ta na cigaba da karbar yan jam'iyyar adawa, yayin da ɗan majalisar Jigawa daga jam'iyyar NNPP ya sauya zuwa sheka a ranar Alhamis.
Wani dan majalisar Sokoto, Hon. Aminu Boza ya ce an gano rikakken dan ta'adda, Bello Turji a gabashin jihar, inda ake zargin ya kakaba harajin ₦25m kan wasu kauyuka.
Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan wasu 'yan bindiga da suka shahara da kai hare hare a Sabon Birni. Wani da aka ceto ya bayyana yadda maboyar ta ke.
Kalaman tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a kan masu koma wa APC sun yi jam'iyyar ciwo, wanda ya jawo aka yi masa zazzafan martani kan sauya sheka.
Yayin da tarun matsaloli suka yi yawa a Arewa, Sheikh Murtala Bello Asada ya ce zai yi wahala Tinubu ya tsallake zabe a 2027 ya danganta hakan da nakasa yankin.
An samu tashin wata mummunar gobara a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke jihar Sokoto. Gobarar ta lalata muhimman kayayyaki.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da zaman lafiya sun samu nasarori kan 'yan ta'adda a jihohin Zamfara da Sokoto. Sojojin sun hallaka kwamandoji masu yawa.
Jihar Sokoto
Samu kari