Jihar Sokoto
Sabuwar kungiyar yan ta'adda mai suna Lakurawa ta ɓulla jihar Sokoto inda ta fara raba miliyoyi domin daukar matasa. Yan ta'addar na daukar matasa a N1m.
Ana fama da matsalar yan bindiga, gwamnatin jihar ta tabbatar da bullar wasu masu alaka ta addini da ake kira Lakurawas da suke ayyukansu a kananan hukumomi biyar.
Sarkin Musulmi a Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya shawarci al'umma kan sukar shugabanni inda ya ce a bar su da Ubangiji ya yi abin da ya ga dama da su.
Sarkin Musulmi, Mai Martaba, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya gwangwaje Farfesa Isa Ali Pantami da sarautar Majidadin Daular Usmaniyya a jihar Sokoto.
Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kama wani jagoran ƴan bindiga, Abubakar Ibrahim wanda aka fi sani da Habu Dogo a jihar Sakkwato.
Rikicin manyan APC a Sokoto ya fara raba kan sarakunan gargajiya a jihar Sokoto. Sarakuna sun fara ajiye aiki suna goyon bayan ɓangaren yan siyasa.
Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya ta ƙaryata jita-jitar rasuwar Mai Martaba, Sultan inda ta bukaci jami'an tsaro su dauki mataki kan masu yada labarin.
Wasu tsagerun ƴan fashin daji sun kai hari kauyen Muridi da ke yankin ƙaramar hukumar Isa a jihar Sakkwato, sun kashe manoma huɗu tare da sace wasu da dama.
Wasu sarakunan gargajiya daga yankin Sokoto da Gabas sun yi murabus da rigimar APC ta yi tsanani domin goyon bayan Sanata Ibrahim Lamido a jihar.
Jihar Sokoto
Samu kari