Jihar Sokoto
Rundunar yan sanda ta kama wani matashi dan shekara 25, Sufyanu Aliyu bisa zargin caka wa matarsa, yarinya yar shekara 16 wuka har lahira a jihar Sakkwato.
Wata kungiyar matasan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bukaci gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya nemi wa'adin mulki karo na biyu a zaben 2027.
Wasu tsagerun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Sokoto. 'Yan bindigan sun kashe wani basarake tare da wasu mutane a yayin harin.
'Yan bindiga sun kakabawa wasu mutane a yankin Bazar na jihar Sokoto harajin N15m. Sun bukaci a sanar da gwamna domin kawo musu dauki kan halin da suke ciki.
Dan majalisar tarayya daga jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da cewa ba zai sake tsayawa takarar Majalisar Wakilai a 2027 ba, domin bai wa matasa dama.
Yayin da Janar Christopher Musa ya bar ofis ba tare da cika alkawarin da ya dauka ba, Bello Turji ya ci gaba da zama tushen kalubalen tsaro a Arewacin Najeriya.
A labarin nan, za a ji cewa masu ruwa da tsaki sun hallara a jihar Sakkwato domin neman yadda za a inganta tsarin almajirci domin yara su daina bara.
Bello Turji ya fara shirya sababbin hare-hare a gabashin Sokoto bayan ruwan damina ya ja baya, an ce ya sake tsara runduna da sauya kwamandoji don karfafa iko.
Duk da janye yajin aikin PENGASSAN, karancin man fetur ya ƙara tsananta a Sokoto, inda farashin lita ya kai ₦970, lamarin da ya janyo tsadar sufuri da wahala.
Jihar Sokoto
Samu kari