Siyasar Najeriya
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo zai jagoranci taron 'yan adawa a Najeriya a Ibadan jihar Oyo. Kwankwaso da sauran yan ADC sun isa Ibadan.
'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun dasa bam a jihar Borno. Bam din ya jawo asarar rayukan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, bayan ya tarwatse.
Kakakin jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdulahi ya zargi jam'iyyar APC da shirya hana taron 'yan adawa a Ibadan. ADC za ta yi taron ne domin shirya tunkarar APC.
Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zabe mai zuwa, mun tattaro muku jihohin Arewa biyar da zabensu zai dauki hankali saboda wasu dalilai a 2027.
A labarin nan, za a ji cewa sanata Abdul Ningi ya dora alhakin matsalar da yan majalisa za su fuskanta yayin zabe mai zuwa a kan rashin aiwatar da kasafin kudi.
Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Gombe ta samu karuwa. Sanatan da ke wakiltar Gombe ta Kudu ya sauya sheka zuwa cikita. Ya gana da Gwamna Inuwa Yahaya.
A labarin nan, za a ji wata ƙungiyar APC ta fara zargin ganawar da Sanata AbdulAziz Yari ya yi da jiga-jigan ADC zai jawo nakasu ga haɗin kan jam'iyya gabanin 2027.
Jam'iyyar APC za ta fara sayar da fom din takara daga 25 ga Afrilu, 2026, sannan za ta gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa a ranar 23 ga Mayu.
Hukumar INEC ta fara shirin zaɓen 2027 a yau 23 ga Afrilu, 2026, inda ta ba jam'iyyun siyasa wa'adin kwanaki 38 domin gudanar da zaɓukan fitar da gwani.
Siyasar Najeriya
Samu kari