Siyasar Najeriya
Shugaban tsagin ADC a Najeriya, Nafi’u Bala ya musanta rahoton da ke cewa ya yi nadamar rikicin jam’iyya tare da zargin rayuwarsa na cikin haɗari.
Tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda a Najeriya, Usman Alkali Baba, ya shiga takarar gwamnan Yobe bayan yarjejeniyar tsayar da ɗan takara guda ta rushe.
Peter Obi ya tabbatar da ficewarsa daga ADC sakamakon rikicin cikin gida, inda ya jaddada cewa har yanzu yana da yakinin samar da sabuwar Najeriya.
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta fitar da jadawalin lokacin gudanar da zaben fidda gwani. Ta bayyana kudaden fom na masu neman takara a inuwarta.
Mai neman takarar kujerar sanatan Kebbi ta Tsakiya karkashin inuwar jam'iyyar APC, Kabiru Sani Giant, ya yi watsi da batun sulhu. Ya ce mutane na son canji.
Tsohon ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa Bola Tinubu ya ba shi izinin barin mukaminsa domin fara shirye-shiryen neman kujerar gwamnan Oyo.
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karyata jita-jitar cewa zai yi takarar shugaban kasa ko kuma yana shirin hada tikiti da Peter Obi.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi na shirin ficewa daga jam'iyyar ADC. Majiyoyi sun bayyana dalilin da ya sa za su yi hakan.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta rahotannin haɗakarsa da Peter Obi gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a Najeriya.
Siyasar Najeriya
Samu kari