Siyasar Najeriya
Bayan da Shugaba Bola Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya na 16, jam'iyyar APC mai mulki ta lashe zabukan gwamnonin jihohi hudu cikin biyar da aka gudanar.
Hadimin Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom, Aniekeme Finbarr a bangaren wayar da kan al'umma ya yi murabus daga mukaminsa domin neman kwarewa a wani sashe.
Gwamnonin jam'iyyar PDP sun bai wa kwamitin gudanarwa watau NWC karkashin Umar Damagum wa'adin watanni uku su kira taron kwamitin zartarwa na ƙasa.
Wasu daga cikin 'yan takarar da suka fafata a zaben gwamnan jihar Ondo, sun nuna goyon bayansi ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa. Sun bayyana cewa sun amince da nasararsa.
Gwamnan jihar Ondo ya kare kansa kan rashin barin Ganduje ya rike takardar shaidar naarar da ya samu a zaben da aka kammala ranar Asabar da ta gabata.
Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta sake ɗage taron kwamitin zartarwa na ƙasa watau NEC wanda ta shirya yi a makon gobe ranar 28 ga watan Nuwamba, 2024.
Wata babbar kotun jiha da ke da zama a birnin Fatakwal ta dakatar da jam'iyyar APC daga gudanar da zabukan shugabanninta. A ranar 19 ga Nuwamba ne ta ba da umarnin.
Tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Cif Bode George ya roƙi Atiku Abubakarz ya hakura da burin zama shugaban kasa, ya koma gefe a zaben 2027.
Injiniya Faozey Nurudeen, wanda ya yi takarar sanata a inuwar Accord Party a zaben 2023, ya bar jam'iyyar, ya ce nan ba da jimawa ba zai sanar da mataki na gaba.
Siyasar Najeriya
Samu kari