Siyasar Najeriya
A labarin nan, za a ji cewa Sanata Kawu Sumaila ya yi tir da kalaman da Sanata Ted Cruz na Amurka ke yi da ake ganin zai iya jefa Najeriya a cikin matsala.
Gwamnatin Sokoto ta nesanta kanta da Mai Shaho bayan wani bidiyo da ya yaɗu. Ta ce ba ta goyon bayan tsafi kuma ta bukaci Hukumar Hisbah ta ɗauki mataki.
An yi sulhu tsakanin Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio, da Sanata Adams Oshiomhole (APC, Edo). An yi hakan bayan Oshiomhole ya zargi Akpabio da karya yarjejeniya.
Abdulsalami Abubakar ya buƙaci INEC ta yi adalci ga dukkan jam'iyyun siyasa yayin da shugaban hukumar ya bada tabbaci kan yin sahihin zabe a 2027.
Atiku Abubakar ya yi watsi da zargin Obasanjo kan cin hanci, yana cewa an tayar da tsohon batu ne domin siyasar zaɓen shugaban ƙasa a zaben 2027.
Northern Christian Progressive group ta yi kira ga APC da Bola Tinubu da su naɗa ɗan siyasa Kirista daga Arewacin Nijeriya a matsayin Darakta Janar (DG) na kamfe.
Gwamnan Abia, Alex Otti, ya ce Hope Uzodimma ba zai iya magana a madadin dukkan gwamnonin Kudu maso Gabas ba kan goyon bayan wa’adin Tinubu na biyu.
Gwamna Seyi Makinde ya ce an gargade shi kan takarar 2027, sannan EFCC ta nemi bayanan kwangilolin Oyo. Ya bayyana hukuncin kotu a matsayin nasarar bin doka.
Ɗan takarar gwamnan Kaduna da ya sha kaye a ADC, Muhammad Bello Mainan Zazzau, ya yi murabus daga jam’iyyar kwanaki bayan sasanta rikicin shugabancinta.
Siyasar Najeriya
Samu kari