Siyasar Najeriya
Sabon shugaban jam'iyyar APC na jihar Rivers, Tony Okocha, ya bayyana cewa muilkin jihar zai dawo hannunsu. Ya nuna cewa jam'iyyar za ta lashe zaben 2027.
Gwamnan jihar Ekiti ya bukaci ƴan siyasar da ke tura masa sakonni ta wayar tarho su dakata haka nan domin babu abin da zai faru sai da izinin Allah.
Babbar kotun tarayya mai zama a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi ta halatta dakatarwar da aka yi wa mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Ali Odefa.
Jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa ta hango haske a zaben gwamnan jihar Osun mai zuwa a 2026, sai dai kalaman ba su yi wa jam'iyyar PDP mai mulki daɗi ba.
Kungiyar matasan Arewa ta bayyana cewa har yanzu yankin na matakin tattaunawa kan sake zaɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a 2027 ko juya masa baya.
Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce alakarsa da Bola Tinubu ya sa har yanzu yaƙe zaune a inuwar APC amma ba don haka ba da ya bar jam'iyyar tun tuni.
Yan siyasa kamar Ali Ndume, Atiku Abubakar, Olusegun Obasanjo Rabi'u Kwankwaso sun rike wuta ga gwamantin Bola Tinubu kan wasu tsare tsaren da ya kawo.
PDP ta koka kan zargin APC na mata Katsalandan a Kano. Ƙusa a PDP, Aminu Wali ya ce su na sane da rikicin da ke damunta. Amma APC ta musanta zargin da ake mata.
Babbar kotu a jihar Benue ta rusa kwamitin da shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya kafa domin magance rikicin APC a Benue. Kotun ta ce Ganduje ya karya doka.
Siyasar Najeriya
Samu kari