Siyasar Kano
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya yi ikirarin cewa APC za ta karɓe Kano a babban zaɓe mai zuwa, ya faɗi haka ne a zauren majalisa.
Sanata Barau Jibrin ya karbi tsohon hadimin Abba Kabir Yusuf a harkar shari'a zuwa APC. Tarin yan NNPP sun sauya sheƙa a shirin kifar da Abba Kabir Yusuf a 2027.
Tsohon ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya gana da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kawu Sumaila a gidansa.
Bisa ga tsarin gudanar da zabe, hukumar KANSIEC ta mika takardun shaidar cin zabe ga zababbun shugabannin kananan hukumomi 44 da kansiloli 484 na jihar Kano.
A karshe dai jam'iyyar NNPP ta yi nasarar lallasa dukkan jam'iyyun adawa a Kano, ta lashe kujerun ciyamomo da kansiloli gaba ɗaya a zsben da aka yi yau Asabar.
Da alamu dai rikicin NNPP ya ɗaba kan manyan jiga-jiganta, taron Dr. Rabiu Kwankwaso da ƴan majalisar tarayya na Kano ya ƙara nuna ɓarakar da ta kunno kai.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kam zaben kananan hukimomin da aka gudanar da jihar. Gwamna Abba ya ce an yi sahihin zabe a jihar.
Tsohon kwamishinan ayyuka a Kano, Mu'az Magaji ya caccaki tsarin yadda jam'iyyar APC ke neman mulki a jihar inda ya ce dole ta bar dogaro da karfin iko daga sama.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mafi yawan wurare da ake gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Kano yan banga ne ke ba da tsaro rike da sanduna da kuma adduna.
Siyasar Kano
Samu kari