Siyasar Kano
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta tarwatsa wasu matasa da suka yi kokarin fasa wuraren adana kaya da wasu shagudan a' Zoo Road' da ke birnin Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gana da sarakuna, malamai da ƴan kasuwa, ya gayyaci masu shirin yin zanga zanga zuwa gidan gwamnatin Kano don su tattauna.
Kungiyar Ja'oji da ke jihar Kano ta fito zanga-zanga domin nuna goyon bayan Shugaba Bola Tinubu inda ta kalubalanci masu fita gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya zabi Manjo-janar Muhammad Inuwa mai ritaya a matsayin kwamishina inda ya tura sunansa Majalisar jihar domin tantancewa.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu matasan karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano sun yi kira ga Sani Danja da ya fito takarar ciyaman din karamar hukumar.
A cikin watan Yuli, jam'iyyar NNPP ta samu koma baya a jihar Kano inda jagorori da magoya baya suka sauya sheka zuwa APC. Sanata Barau Jibrin ne ya karbe su.
Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun fice daga NNPP zuwa APC a jihar Kano. Rabi'u Daushe, Hauwa Waraka, Alhaji Habu Tabule na cikin wadanda Barau Jibrin ya karba.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Doguwa, ya bayyana cewa jihar na bukatar kudi har N60 biliyan domin gyara bangaren ilimi tare da samar da kayayyaki.
Wata mata ta yi zargin cewa shugaban jam'iyyar NNPP, na karamar hukumar Dawakin Tofa, ya yiwa wata mata dukan tsiya a gidan gwamnatin jihar Kano.
Siyasar Kano
Samu kari