Siyasar Arewa
A labarin nan, za a ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana cewa taron PDP da aka gudanar a jihar Oyo ba komai ba ne face taron nishadi.
Wasu jiga jigan APC a Zamfara sun maka shugaban jam'iyyar a kotu bisa zargin an dakatar da su ba bisa ka'ida ba. Sun gabatar da bukatu akalla hudu gaban kotu.
Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya kwatanta jam’iyyar APC da jirgin Annabi Nuhu, yana cewa ita ce kadai hanyar ceto Najeriya, lamarin da ya jawo martani masu zafi.
Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, da Shugaban APC na kasa, Prof. Nentawe Yilwatda, sun karɓi daruruwan masu sauya sheƙa daga jam’iyyu biyar zuwa APC a Plateau.
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Idris Wada, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP, inda ake sa ran Gwamna Usman Ododo zai tarebe shi a ranar Litinin.
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya sanar da cewa zai sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC a hukumance ranar Laraba, 19 Ga watan Nuwamba, 2025.
A labarin nan, za a ji yadda wasu mata da suka buga gwagwarmaya a siyasar jihohinsu suka sha kasa a zaɓukan gwamnoni bayan sun tsaya takara a jam'iyyu daban-daban.
An kashe tsohon dan takarar Majalisar Tarayya, Hon. Umar S. Fada Moriki, a kan hanyar Tsafe, lamarin da ya tayar da hankalin al’ummar Zamfara baki ɗaya.
Mutum ɗaya ya mutu, shida sun ji rauni a turmutsutsin da aka samu a gidan Ministan Tsaro, Bello Matawalle a Gusau. An ce lamarin ya faru ne a ziyarar ministan.
Siyasar Arewa
Samu kari