Siyasar Arewa
Gwamna Caleb Mutfwang na Plateau ya fice daga jam’iyyar PDP; zai shiga APC a hukumance ranar Juma’a domin haɗa kai da gwamnatin tarayya don ci gaban jihar Plateau.
Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya fice daga jam’iyyar PDP a hukumance, yana cewa yana bukatar shugabanci mai maida hankali da ingantaccen aiki.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya roƙi al’ummar jihar su yafe masa duk wanda ya ɓata masa rai a cikin shekaru bakwai na mulkinsa.
A labarin nan za a ji cewa jam'iyya mai mulki a Kano, ta sanar da dakatar da Alhaji Sammani Ungogo daga Shugaban dattawan yankin kan kin bin umarni.
Mambobi 6 na majalisar dokokin Zamfara sun sauya sheka daga PDP zuwa APC, saboda rikice-rikicen cikin gida da dakatar da su da majalisa ta yi ba bisa ƙa'ida ba.
Babban lauya Sebastine Hon ya ayyana kudirin tsayawa takarar gwamnan Benue a 2027, inda bayyana shirin karbar mulki daga hannun Gwamna mai ci Hyacinth Alia.
Karamar Hukumar Kirikasamma a Jihar Jigawa ta fara biyan alawus na wata-wata ga tsofaffin shugabanninta da kansiloli domin karfafa hadin kai bayan sun bar ofis.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sallami hadimansa guda hudu nan take bisa dukan kansilan Shamaki da ya bayyana a bidiyo mai yawo.
Jam’iyyar PDP a Jigawa ta soki dakatar da tsohon gwamna Sule Lamido daga kwamitin amintattu, tana cewa matakin yana barazana ga hadin kan jam’iyya.
Siyasar Arewa
Samu kari