Shugaban Sojojin Najeriya
A wannan labarin, za a ji cewa daya daga cikin masu jan tawagar 'yan ta'adda, Babawo Badoo ya koma ga Mahaliccinsa bayan ya yi kokarin kwace makamin sooja.
Tun daga 1966 aka fara juyin mulki a Najeriya. An kashe Tafawa Balewa da Sardaunan Sokoto a juyin mulki. Wasu juyin mulkin ba su yi nasara ba a Najeriya.
Kungiyoyin shiyyoyin a kasar nan sun yi Allah wadai da duk wani tunani da zai kai ga batun juyin mulki a Najeriya, suna cewa zai zama koma bayan gaske.
Ana bincken tsohon gwama daga Kudancin Najeriya kan zarginsa da hannu a shirya wa shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki. An kama wasu sojoji kan lamarin.
Ana fargabar Boko Haram ta kashe kwamandan bataliyar soji ta 202, sojoji biyar da ’yan CJTF uku a Kashimiri, Borno; sojoji na ci gaba da aikin kakkabe miyagun.
Sojojin Najeriya sun ceto mutane 21 da aka sace, ciki har da ‘yan kasar China hudu, a wani farmaki na Operation FANSAN YAMA a jihohin Kwara da Kogi.
Hedikwatar Tsaron Ƙasa ta karyata labarin soke bikin cika shekara 65 da samun ‘yancin kai da cewa ana yunkurin juyin mulki ne a Najeriya inda ta ce karya ne.
Ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya ziyarci Leonardo a Italiya, inda ake kera jiragen yakin sojojin saman Najeriya domin ingnta tsaro da sabunta kayan aiki.
Rundunar sojin Najeriya ta ceto wasu mutane 21 da 'yan bindiga suka sace a jihohin Kwara da Kogi. Dakarun sojin sun bayyana cewa wasu daga cikinsu sun kasa tafiya.
Shugaban Sojojin Najeriya
Samu kari