
Shugaban Sojojin Najeriya







Darektan harkokin yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya ce ba bam ya kashe mutane ba. Janar Buba ya ce an yi nasara ba a yi barna sosai ba.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya mika ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar gwamnan Jigawa, Hajiya Maryam da babban dansa, AbdulWahab Umar Namadi.

Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tuntubi hukumomin soji domin bincike kan kuskuren kashe fararen hula a kauyuka.

Rundunar sojojin Najeriya ta dora alhakin harin da jami'anta na sama su ka kai kauyuka biyu da ke jihar Sakkwato, wanda ya jawo asarar rayuka akalla 10.

Rundunar sojin saman Najeriya watau NAF ta ce jirgin sama bai kai farmaki ba sai da aka tabbatar da wuraren biyu na da alaƙa da ƴan Lakurawa a jihar Sakkwato.

Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya kai ziyara kauyukan da ake zargin jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta bisa kuskure, ya ba da tallafin Naira miliyan 20.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba zai binciki hafsoshin tsaro ba kan yadda suke kashe kudaden da aka ware musu domin yaki da ta'addanci.

Sojojin kasar nan sun yi babban kamen miyagun 'yan ta'adda.. Hedkwatar tsaron ta tabbatar da cafke wasu manyan 'yan ta'adda a Arewa. DHQ ta fitar da sunayen miyagun.

Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargi da jigilar makamai a jihar makamai. Sojojin sun kwato alburusai masu yawa.
Shugaban Sojojin Najeriya
Samu kari