Sabon Farashin Man Fetur
A labarin nan, mun wallafa cewa fitaccen dan kasuwa a Najeriya, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana shakku a kan shakkun kan aikin matatun gwamnatin tarayya.
Tare da hadin gwiwa da gwamnatin jihar Ondo, kamfanin BINL zai gina matatar man fetur ta dala biliyan 15, sannan zai gina kasuwar cinikayya ta FTZ a jihar.
Matatar Dangote za ta daina shigo da danyen mai nan da Disamba 2025 daga waje, inda za ta dogara kan mai na cikin gida, don rage matsin Naira da farashin fetur.
Matatar Dangote ta rage farashin man fetur a fadin Najeriya zuwa N820 daga N840. Sauke farashin fetur ya biyo bayan saukar farashin danyen mai a duniya.
Gwamnatin Najeriya ta amince da gudanar da taro na musamman kan farashin man fetur. Za a yi taron a ranakun 23 da 24 ga watan Yuli karkashin NMDPRA.
Yan kasuwa sun ki su rage farashin litar man fetur a gidajen mansu duk da matatar Ɗantoge ta yi rangwamen N40, sun ce suna da tsohon kaya da suka saya da tsada.
Matatar man hamshakin ɗan kasuwa, Aliko Ɗangote ta rage farashin fetur a karon farko bayan gangar mai ta sauka sakamakon tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran.
Rahotanni daga jihar Legas sun nuna cewa gidajen mai mallakin kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL sun kara farashin kowace litar man fetur zuwa N925.
Farashin mai ya faɗi da kusan 5% bayan Isra'ila ta amince da tsagaita wuta da Iran. Kasuwannin duniya sun farfaɗo. Brent ya dawo $69, yayin da WTI ya koma $66.14.
Sabon Farashin Man Fetur
Samu kari