
Sabon Farashin Man Fetur







Matatar Dangote ta sayi danyen man Ceiba har ganga 950,000 daga kasar Equatorial Guinea, yayin da NNPC ke tattaunawa da matatar kan tsarin sayen danyen mai da Naira.

Sabon farashin fetur daga matatar Dangote ya sa ‘yan kasuwa sun kauce wa manyan rumbun ajiya na masu zaman kansu, yayin da ake sa ran ci gaba da saukar farashin.

Yan kasuwar man fetur sun bayyana cewa za su sauke farashin man fetur kasa da na matatar Dangote. Hakan na zuwa ne bayan mai ya sauka a kasuwar duniya.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce an cire tallafin man fetur ne domin kare goben Najeriya. Ya fadi haka ne yayin kaddamar da taron matasan Najeriya a Abuja.

Kungiyar dillalan mai ta PETROAN ta nemi a kafa doka da za ta kayyade sauya farashi zuwa sau daya cikin watanni shida domin hana rashin tabbas a kasuwa.

Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya dauki matakin daina sayar da danyen man fetur ga matatun cikin gida a Najeriya. Wannan matakin zai sa fetur ya yi taada.

Masana harkokin tattalin arziki sun yi hasashen cewa za a iya ƙara samun sauƙi a farashin litar mai idan gangar ɗanyen mai ta ci gaba da sauka a kasuwannin duniya.

Wani masanin tattali a Najeriya ya bayyana cewa farashin man fetur zai cigaba da sauka a Najeriya har zuwa watan Yunin 2025 bayan Dangote da NNPCL sun rage kudi

Kungiyar masu dillancin kan feturi a Najeriya watau PETROAN ta nuna farin ciki da yabon NNPC da Ɗangote bisa rage farashin litar man fetur a Najeriya.
Sabon Farashin Man Fetur
Samu kari