Muhammadu Sa'ad Abubakar
Gamayyar kungiyoyin Musulmi a Najeriya sun gargadi gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu kan cigaba da girmama mai alfarma Sarkin Musulmi a matsayinsa na jagora babba.
Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu, yasa hannu kan yi wa dokar masarautu a jihar kwaskwarima. Hakan ya hana Sarkin Musulmi ikon nada hakimai da dagatai baki daya.
Majalisar kolin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta yi kira ga yan siyasa kan girmama sarakuna musamman wadanda suke rike da jaggorancin addini a cikinsu.
Malamai a Arewacin Najeriya sun bayyana cewa, ba za su amince ba a taba martabar Sakin Musulmi alhali suna kallo. Sun bayyana matsayarsu kan ci gaba da mulkin.
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya tube sarakuna akalla 15 bayan hawansa karagar mulkin jihar tare da kirkirar sabuwar doka da za ta rage ikon Sultan.
Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa mai alfarma Sarkin Musulmi bai da ikon nada kowa a idon doka. Ta ce hakan ya sanya za ta yiwa doka gyara a jihar.
Fadar Sarkin Musulmi ta fito ta yi magana kan batun rikicin da ake yadawa tana yi da gwamnatin Sokoto. Fadar ta ce babu wata rigima a tsakanin bangarorin biyu.
Yayin da ake kokarin gyaran fuska a dokar masarautun jihar Sokoto, yau Talata za a fara sauraran ra'ayin jama'a game da sabuwar dokar da ake magana a kai.
Cibiyar dabbaka shari'ar Musulunci ta gargadi gwamnatin jihar Sokoto kan wasa da iko da kuma darajar da Sultan ke da shi musamman a idon Musulman Najeriya.
Muhammadu Sa'ad Abubakar
Samu kari