Haduran mota a Najeriya
Rahotannin da muka samu da safiyar Litinin ya nuna cewa wani bene mai hawa 2 ya ruguje a layin Amusu da ke jihar Legas, hukumar LASEMA ta ce abin ya zo da sauki.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana yadda hatsarin motan da ya ritsa da dan tsohon gwamnan jihar Kaduna. Faisal Ahmed ya rasu ne a ranar Asabar.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta haramta wa hukumar bincike da kula da zirga-zirgar ababen hawa (VIO) kwacewa ko kuma cin tarar masu ababen hawa.
Hadarin mota ya ritsa da yan Maulidi a jihar Jigawa. Mutane shida sun rasu guda tara sun samu munanan raunuka. Rundunar yan sanda sun fara bincike kan hadarin.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar wani hatsari wanda ya lakume rayukan wasu mutane shida 'yan gida daya. An ce mota ce ta kwacewa direba.
Ana fargabar mutane hudu da suka hada da wata mai shayarwa sun mutu a Gusau, jihar Zamfara bayan da wata motar tirela ta murkushe su a lokacin da suke kan babura.
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja sun nuna cewa tankar mai maƙare da fetur ta fashe ta kama da wuta a Maitama da ke birnin tarayya Abuja, mutane sun ji raunuka.
An yi mummunan hadarin mota a jihar Ogun inda mutane 18 suka kone kurmus bayan motar ta kama da wuta. Matukin motar na kwance a asibiti saboda raunuka.
A wannan labarin, gwamnan Kaduna, Uba Sani ya mika ta’aziya ga iyalan wadanda su ka rasu a hadarin mota da ta afku a Saminaka da ke karamar hukumar Lere.
Haduran mota a Najeriya
Samu kari