Haduran mota a Najeriya
Hukumar kiyaye haɗurra reshen jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar fasinjoji 10 a wani mummunan hatsari da ya auku da asubahin ranar Talata, 12 ga watan Disamba.
An bayyana yadda wasu mutane suka mutu a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadi, Atiku ya shiga damuwar da ta sa ya fito ya yi magana a kan wannan lamarin.
Wani mummunan hatsarin mota ya salwantar da rayukan mutum 16 a kan titin hanyar Kaduna zuwa Abuja. Mutane da dama sun samu munanan raunuka a hatsarin.
Iyalan dalibin jami'ar jihar Ebonyi da ayarin motocin gwamnan jihar Ebonyi suka halaka na neman ayi musu adalci yayin da yan sanda ke yin rufa-rufa.
Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa babbar gadar Alapere ta rushe sakamakon wata tirela dauke da kwantena da ta hau kanta. Hakan ya shafi gadar mainland.
An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota wanda ya ritsa da matafiya a jihar Cross Rivers. Hatsarin ya salwantar da rayukan mutum biyar sannan wasu sun jikkata.
Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da wasu motoci biyu a jihar Oyo. Matafiya da dama sun samu raunukan kuna a hatsarin da ya auku cikin tsakar dare.
An samu asarar rayukan bayin Allah bayan aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar Kwara. Mutum 25 sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu suka raunata.
An samu asarar rayuka a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Kebbi. Hatsarin wanda ya ritsa da motar tirela ya salwantar da rayukan mutum 11.
Haduran mota a Najeriya
Samu kari