Jihar Rivers
Dattawan jihar Rivers sun ja kunnen Wike inda suka ce ya tabo stuliyar dodo tun da ya tabo tsohon gwamnan jihar Peter Odili. Sun bukaci Wike ya ba Odili hakuri.
Gwamnan jihar Rivers, Suminalayi Fubara ya jijjige Wike da mutanensa. Gwamnan ya ce ya dogara ga Allah wajen maganin makiya jihar da al'ummarta a gaba.
Gwamnan jihar Rivers ya gabatar da kasafin kudin sama da Naira triliyan 1 na shekarar 2025. Siminalayi Fubara ya ce kasafin N1.888tn zai bunkasa jihar a 2025.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana fatan cewa APC za ta ci gaba da lashe jihohi a Kudu maso Kudu, yana mai cewa zai kawo sauyi mai kyau.
Gwamnonin jihohin Rivers da Bayelsa sun kawo karshen rikici kan rijiyar mai da aka shafe shekaru 22 ana yi a tsakaninsu wanda suka yi yarjejeniyar janyewa daga kotu.
Wata kotu a Rivers ta sauke shugannin APC da ke yi wa bangaren Abdullahi Ganduje biyayya bayan sun shirya zabe ba bisa ka'ida ba, an zargi Ganduje da rashin gaskiya
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya caccaki tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus inda ya fadi dalilin da yasa ya haɗa baki aka cire shi daga mukaminsa.
Gwamnan jihar Ribas ya rattaba hannu tare da umartar a bai wa ma'aiksta da ƴan fansho alawus na N100,000 domin su yi shagalin bikin kirsimeti cikin walwala.
Kungiyoyin fararen hula sun hada tawaga ta musamman mai mutane 50 domin gano gaskiya kan halin da matatar NNPCL ta Fatakwal ke ciki ga yan Najeriya.
Jihar Rivers
Samu kari