Kungiyar Manoman Shinkafa
Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya ce gwamnatinsa za ta siyo shinkafa ta siyarwa al'ummar jihar kan farashi mai rahusa, tsofaffi da faƙirai kuma za a basu kyauta.
Majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC) ta amince da rabawa manoma takin zamani tare da kuma kaddamar da dakarun gona don yaƙi da 'yan ta'adda da ke farmakar manoma.
Bola Tinubu ya ce a fito da shinkafa, masara ton 102, 000, 000, a rabawa talakawa. Ministan labarai ya sanar da matsayar da aka cin ma bayan zaman su a Aso Villa.
Gwamnatin jihar Kebbi tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya sun shirya farfado da harkar noma a jihar. Gwamnatin za ta ba manoman rani man fetur kyauta.
Gwamnatin jihar Katsina ta tallafawa manoma 2,040 da kayan noman rani da suka hada da injinan ban ruwa a wani shiri da take yi na bunkasa sana'ar noman rani a jihar.
Wasu tsagerun yan bindiga sun tarfa wasu manoma biyu a gonakinsu a yankin Yangtu da safiyar ranar Talata a jihar Taraba sun yi ajalinsu, mutane sun ruɗe.
Tsohon Shugaba Obasanjo ya ba Gwamnati shawarar tattalin arziki, ya bukaci a haramta shigo da kaya daga kasar Sin domin a iya inganta masana’antun da ke gida.
Wasu daga cikin mutanen da su ka ci gajiyar lamunin Korona sun koka kan yadda bankin CBN ke kwashe musu kudade a kokarin kwato kudaden daga mutane.
Gwamnatin Adamawa ta kare kanta dangane da matakin sanya hoton gwamna Ahmadu Finfiri a jikin buhunan shinkafar tallafin rage zafin cire tallafin man fetur.
Kungiyar Manoman Shinkafa
Samu kari