Rabiu Kwankwaso
Jam'iyyar NNPP ta musa ikirarin da Shugaban APC, Abdullahi Ganduje na cewa Rabiu Kwankwaso zai koma APC bayan mutuwar NNPP. NNPP ta ce zancen ba gaskiya ba ne.
Hoton da ake yaɗawa na Rabiu Kwankwaso sanye da hula mai ɗauke da tamabarin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba gaskiya ba ne, kirkirarsa aka yi.
Shugaban APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas ya ce kofar jam'iyyar a bude take ga kowa, musamman ga masu kishin kasa da ci gaba inda ya yi gargadi da gindaya sharuda.
Dattijon NNPP, Buba Galadima ya bayyana cewa babu yadda za a yi jagoran Kwankwasiyya na kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya hada inuwa guda da Abdullahi Ganduje.
Shugaban tsagin NNPP a Kano, Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa ya ce sun san da ganawar Abdullahi Ganduje da 'yan majalisar jam'iyyar da suka hada da Kawu Sumaila.
Sakataren yada labaran APC na Kano, Ahmed S Aruwa ya bayyana cewa komawar Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar zai haddasa rikici da tarwatsa 'ya'yanta.
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso zai dawo APC saboda NNPP ta mutu murus a Najeriya. Ganduje ya ce masu shirin hadaka za su wargaje.
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah wadai da harin da ƴan bindiga suka kashe gomman mutane a Filato.
Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya ce za su maraba da Rabiu Kwankwaso idan ya sauya sheka zuwa APC da magoya bayansa.
Rabiu Kwankwaso
Samu kari