Jam'iyyar PDP
Jam'iyyar APC mai mulki ta lashe zaben da aka gudanar a jihohin Kano, Ekiti, Nasarawa, Ondo, Ekiti da Enugu. Jam'iyyar PDP ta lashe kujerar jihar Rivers.
Jigo a jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya yi hasashen cewa Shugaba Tinubu na iya lashe jihohi kusan 22 a zaben shugaban kasa na zaben shekarar 2027.
Tsagin jam'iyyar PDP da ke karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, ya gabatar da dan takarar gwamna a Gombe. Hakan na zuwa ne an ba Pantami takarda.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayar da shawarwari ga 'yan takarar jam'iyyar PDP a zaben 2027. Ya bukaci su tashi tsaye.
Tsagin jam'iyyar PDP ya bai wa yan takarar gwamnan da aka amince da su shaidar takara ciki har da tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami a taron NEC.
Jam'iyyar PDP ta ce ministan Abuja Nyesom Wike ba zai koma APC na dindindin ba, tana mai cewa yana cikin gwamnatin APC ne a matsayin “aro” kawai.
Tsohon hadimin gwamnan jihar Gombe, Aliyu Musa, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP. Ya nuna goyon bayansa ga takarar Farfesa Isa Ali Pantami.
Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti ya sake lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar 20 ga watan Yunin 2026 inda ya doke PDP, LP, ADC da sauransu.
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta ayyana ɗan takarar PDP, Olaka Nwogu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbin sanatan Rivers ta Kudu maso Gabas.
Jam'iyyar PDP
Samu kari